1. Cin amana yana daga cikin Halayen munafurci. Manzon Allah (saw) ya lissafta wasu halaye guda uku, yace duk wanda yake dasu acikin halayensa, to hakika shi munafiki ne. Koda yayi sallah yayi Azumi, koda yayi Hajji yayi Umrah, koda yace Shi Musulmi ne (Subhanallah!!!).
2. CIN AMANA yana daga cikin abubuwan da suke Tauye Imanin Mutum. Mutukar mutum zai rika cin amanar Mutane, to kullum Imaninsa raguwa yake yi.
3. CIN AMANA yana daga cikin halayen da suke Qaskantar da darajar mutum awajen Allah. Mutukar mutum bai rike amanar bayin Allah ba, to Allah ne zai zama abokin rigimarsa aranar Alqiyamah (Subhanallah!!!).
4. CIN AMANA yana sanya mutum yayi baqin jini acikin al'ummah, darajarsa da mutuncinsa su zube, sannan kuma al'ummah su rika gudunsa.
5. CIN AMANA yana zama sanadiyyar Dulmiyar mutum acikin wutar Jahannama. Kamar yadda yazo acikin hadisi, Allah zai sanya amanar acikin chan Qasan Wutar Jahannama, sannan a umurci Maciyin amana cewa ya shiga ya dauko-ta
Sai ya dauko ya hauro wani babban Tudu, sannan sai ita kuma Amanar ta subuce ta koma chan Qasan ramin Jahannama. Sai Mala'iku su daka masa Tsawa suce ya koma ya daukota. Haka zai yi ta yi har Illa ma sha'Allahu.
6. CIN AMANA yana zubar da albarkar dukiya. Domin kuwa komai yawan kudi, in dai aka chudanyashi da kudin Cin amana sai ya lalace.
Yaku Jama'a!!! Ya Zama Wajibi mu rika kiyaye amanar junanmu don samun mutunci awajen Allah da bayin Allah.
ALLAH YA BAMU IKON KIYAYEWA
08028627133