TAMBAYOYIN DA BAI KAMATA A MATSAYINMU NA MUSULMAI MUDINGA YAWAITA TAMBAYA BA


Wani matashi ya tambayi abokinshi, ina kake aiki?

Sai ya Fadamasa.Sannan kuma yakara cewa nawa ake biyanka a kowane wata? Sai yafada mai dubu biyar(5000)

Sai abokin yace : 500 kadai? Tayaya zaka rayu da dubu biyar? 

Tun daga wannan lokacin ya fara jin ya raina aikinshi, yaje ya nemi a qara mashi albashi, mai gidan yaqi qara mashi, tundaga nan kuma ya watsar da aikin.A da yana aiki, yana samun 5000 a wata, amma yanzu baya aikin komai.



Wata ta tambayi qawarta wace kyauta mijinki yaba yimiki a ranar birthday dinki?

Sai tace bai baya bani komai.

Sai qawar tace: Da gaske kike? Anya kina da daraja a wurinshi kuwa? 

Bayan ta samata shakku a ranta ta tafi, da mijin matar nan ya dawo ya tadda ta cikin fushi, suka hau rigima da jayayya daga qarshe ya sake ta.

Daga ina matsalar ta fara? Daga wannan kalmar da qawarta ta gaya mata.

Ance akwai wani mahaifi da yake rayuwa cikin kwanciyar hankali da iyalanshi,  sai abokinshi yace mashi, ya akai danka bai ziyartarka sosai? Anya rashin lokaci ne ko ko dai baya sonka?

Tun daga wannan rana kwanciyar hankalin mahaifin ya qare, ya dawo kallon dukkan abunda danshi yakeyi a matsayin aibi da kuskure, kullum cikin damuwa da rashin godiyar kyautatawar da dandanshi yake mashi.

Tambayoyi ne da zamu iya tsammanin daidai suke, saidai suna iya rusa zamantakewa.

Meyasa baka sayi babbar waya ba?

Meyasa baka mallaki mota ba?

Tayaya zaka riqa jure halayen wannan mutumin?

Tayaya zaka bari ana yi maka wannan abun?

Muna yin wadannan tambayoyin la'alla bisa rashin sani, ko son jin labari, saidai bamu sani ba zasu iya haifar da wasu tambayoyin a zuciyar mai sauraro.

Abunda saqon ya qumsa shine : Karka zamo cikin masu rusa katangar alaqar da take ginanna.

Ka shiga gidan mutane a makance, ka fito a kurmance, babu ruwanka da aibobin cikinsa.

Ba ina wanke kaina bane a lokacin da nake isar da wannan saqon...kuma ba ina nufin ni bana kuskure bane.

Kawai dai nasiha ce nake aikawa zuwa garemu baki daya.

Allah Yasa Mufadaka, Ameeeen.

Post a Comment

Previous Post Next Post