1- Arzikinka waninka ba zai ci maka ba, duk inda kake sai arzikinka ya biyoka, saboda haka babu bukatar ka hana kanka sukuni a kan abin da Allah bai kaddara maka ba.
2- Aikinka babu Wanda zai yi maka, saboda haka sai ka dage wajen yi wa Allah biyayya domin Allah ba zai baka sakamakon abin da baka aikata ba.
A rayuwa kowa ta kanshi ya keyi, kayi kokari ka aikata abin da zai amfaneka duniya da lahira.
Ya Allah ka bamu dama da ikon aikata alheri Bijahi Rasulillahi (S.A.W) .🙏🙏🙏
Ya Allah Yakara Yima Sarkin Musulmi Jagora Akan Wannan Jagoranchin da Allah Yabashi Alfarmar Annabi da Alqur'ani 🤲🤲
Ina Muku Fatan Alkhairi Da Kuma Barka Da Safiya. 🙏🙏🙏