SANYA HIJABI GA MACE, WAJIBI NE AKAN MACE IDAN ZATA FITA UNGUWA TA SANYA HIJABI



Daga cikin abubuwan da suke karawa mace kima da daraja akwai sanya hijabi, hijabi da ya cika sharuddan hijabi na Musulunci,babu wata mace da zata sanya hijabi dan Allah face Allah ya kara daukaka ta ya kuma kara mata kwarji ni da daraja a idanuwan masu imani,kuma zata sami kariya ta musamman daga wajan Allah.


Wajibi ne akan kowace mace musulma mai imani mai biyayya ga umarnin Allah da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama,ta sanya hijabi duk lokacin da zata fita ko zata yi magana da waɗanda ba maharramanta ba, saboda Allah ne da kansa yayi umarnin da hakan .


Allah Ta'ala yana faɗa ga Matan Annabi ﷺ :

 *﴿وإذا سألتموهن متاعا فاسألوهن من وراء حجاب ذلكم أطهر لقلوبكم وقلوبهن﴾*

Ma'an

{idan zaku tambaye su wani ,to ku tambaye su ta bayan hijabi,hakan yafi tsarkaka ga zukatan ku da zukatan su}.


Idan har Matan Manzon Allah ﷺ da girman darajar su da matsayin su,amma duk da hakan Allah ya umarce su da sanya hijabi duk da su ne mafi alheri matan dukkan al'umma,ina ga sauran mata musamman matan yanzu.?


Yan mata yan uwana wallahi musulunci ya mutunta ki da ya umarce ki da sanya hijabi, hijabi shine mutuncin ki, darajar ki, da kuma kimarki.


Allah sa Mudace, mu kuma fi ƙarfin zukatan mu.

Post a Comment

Previous Post Next Post