DUK YADDA KAKE DA JARABAR SABON ALLAH TO KA KIYAYI WADANNAN




1- Kada ka yarda kayi shirka da Allah ko kafirci, babba ne ko karami, domin suna da hadari sosai.


2- ka nisanci bidi'a matukar nisanta, domin zaka koma abubuwan ibadar ka zasu koma na zunubi.


3- kada ka kuskura ka yi yunkurin halatta abinda kake aikatawa marar kyau.


4- ka nisanci takama da bayyana sabon Allah a fili.


5- kada ka yadda kayi aikin sabon da zunubin sa zai rika gudana ko bayan ranka.


6- ka nisanci duk zunubin da ke da alaka da hakkin wani, domin yana da wahalar kankarewa.


7- kada ka yadda ka rena aikin zunubi, ka kalli girman wanda ka sabama.


8- ka yawaita istigfari da nadama, da fatan daina aikin sabo ko wane iri ne.


Dr Imrana Usman Bukkuyum (H)

1 Comments

Previous Post Next Post